Majalisar Dokokin Hungary Ta Amince Da Matakin Tsige Shugaban ƙasar, Tamas Sulyok.

Majalisar Dokokin Hungary Ta Amince Da Matakin Tsige Shugaban ƙasar, Tamas Sulyok.

Majalisar Dokokin ƙasar Hungary ta amince da wani gyaran kundin tsarin mulki da zai cire Shugaban ƙasar, Tamas Sulyok daga mukaminsa, a wani babban mataki na sauya tsarin mulki da sabuwar gwamnati ke aiwatarwa.

Kudirin ya samu amincewa da ƙuri'u 139, yayin da 'yan majalisa shida kacal suka ƙi amincewa da shi. Matakin zai kawo ƙarshen wa'adin shugabancin Sulyok tare da bai wa majalisar damar zaɓen sabon shugaban ƙasa.

Fira Minista Peter Magyar, wanda jam'iyyarsa ta Tisza ta kayar da jam'iyyar Fidesz ta tsohon Fira Minista Viktor Orban a zaɓen watan Afrilu, ya sha alwashin rage tasirin jami'an da aka naɗa a lokacin mulkin Orban.

Sabbin sauye-sauyen kundin tsarin mulkin sun kuma haɗa da gyaran tsarin shari'a da kafa wata hukuma mai binciken zargin almundahanar kuɗi a gwamnatin da ta gabata, da kuma sanya iyakar wa'adin shekaru 12 ga 'yan majalisa.

Shugaba Sulyok na da kwanaki biyar ya rattaba hannu kan kudirin domin ya zama doka. Idan ya ƙi sanya hannu, gwamnati ta bayyana cewa majalisar za ta fara shirin tsige shi daga mukaminsa.

Ko da yake mukamin shugaban ƙasar Hungary na da ƙarancin ikon gudanarwa, yana da ikon amincewa da dokoki ko kuma tura su zuwa Kotun Tsarin Mulki domin a sake duba su. Gwamnatin ta ce waɗannan sauye-sauyen na da nufin ƙarfafa dimokuraɗiyya da kuma gaggauta aiwatar da shirinta na gyaran ƙasa.

0 $type={blogger}: