Gwamnatin Kano Ta Bai Wa Iyalan Jami'in Ƴan Sanda da Ya Rasu a Bakin Aiki Tallafin Naira Miliyan Ɗaya da Kayan Abinci.

Gwamnatin Kano Ta Bai Wa Iyalan Jami'in Ƴan Sanda da Ya Rasu a Bakin Aiki Tallafin Naira Miliyan Ɗaya da Kayan Abinci.

Gwamnatin Jihar Kano ta bai wa iyalan marigayi Sufeto Sani Haladu, wanda ya rasu yayin gudanar da aikinsa a ranar 27 ga Maris, 2026, tallafin kuɗi na Naira miliyan ɗaya tare da kayan abinci.

Kayan tallafin sun haɗa da buhunan shinkafa biyar da buhunan taliya guda shida da buhunan makaroni guda shida, da galan biyu na man girki mai lita 25-25. 
An miƙa tallafin ne a hedikwatar Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta hannun Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Mohammed Tajo Othman, a madadin gwamnatin jihar.

Da yake karɓar tallafin a madadin Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda mai kula da Ayyuka, Lawal Isa Mani, ya yabawa gwamnatin jihar bisa wannan kyakkyawan mataki.

Ya bayyana marigayi Sufeto Sani Haladu a matsayin jajirtaccen jami'i mai biyayya da sadaukarwa, wanda ya rasa ransa yayin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan tallafi, yana mai cewa hakan zai ƙara wa jami'an tsaro ƙwarin gwiwa tare da nuna cewa ana daraja sadaukarwar da suke yi.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tallafa wa iyalan marigayin, sannan ya buƙaci jami'an 'yan sanda su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da jajircewa. 
Haka kuma ya roƙi al'ummar jihar da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin ƙarfafa tsaro a faɗin Kano.

0 $type={blogger}: