IRGC Ta Ce Ta Kai Hari Kan Hedkwatar Rundunar Sojin Ruwa Ta Amurka a Bahrain Da Kuma Sansanin Soji a Jordan

IRGC Ta Ce Ta Kai Hari Kan Hedkwatar Rundunar Sojin Ruwa Ta Amurka a Bahrain Da Kuma Sansanin Soji a Jordan

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan wasu cibiyoyin sojin Amurka a Bahrain, ciki har da hedkwatar Rundunar Sojin Ruwa ta Biyar (US Fifth Fleet), da kuma wani sansanin sojin Amurka a Jordan.

A cikin jerin sanarwar da ta fitar ranar Talata, IRGC ta ce rundunar ruwanta ta kai hari kan rumbunan makamai da cibiyoyin sadarwar tauraron dan adam da wuraren kwanan sojojin Amurka da kuma na'urorin radar a Bahrain.

Har ila yau, rundunar ta ce bangaren Rundunar Sojin Sama ya kaddamar da hare-haren hadin gwiwa ta amfani da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuƙa, inda ta yi ikirarin kai hari kan hedkwatar Rundunar Sojin Ruwa ta Biyar ta Amurka da rumbunan man fetur da kuma wasu na'urorin kariyar sararin samaniya.

IRGC ta kuma ce ta harba makamai masu linzami kan wani muhimmin sansanin sojin Amurka da ke Jordan, tana zargin cewa ana amfani da sansanin wajen kai hare-hare cikin Iran. 
Ta jaddada cewa hare-haren sun shafi wuraren sojin Amurka ne kawai, ba al'ummar Jordan ba.

Rundunar ta ce hare-haren na daga cikin martanin da take ci gaba da mayarwa kan abin da ta kira take-taken Amurka, duk da yarjejeniyar fahimtar juna da Pakistan ta shiga tsakani wajen samarwa domin rage rikici.

A lokacin wallafa wannan rahoto, Amurka ba ta fitar da wata sanarwa kan ikirarin Iran ba, kuma ba a samu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da faruwar hare-haren ko irin barnar da aka yi ba.

Lamarin na zuwa ne yayin da rikici tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙamari, musamman dangane da tsaron mashigar ruwan Hormuz da kuma tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.

0 $type={blogger}: