Isra'ila Ta Gargadi Trump Kan Zargin Shirin Iran Na Kashe Shi.

Isra'ila Ta Gargadi Trump Kan Zargin Shirin Iran Na Kashe Shi.

Isra'ila ta sanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, cewa tana da bayanan sirri da ke nuna Iran na shirin kai masa hari da nufin kashe shi, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka suka ruwaito.

Har yanzu dai gwamnatin Amurka da ta Iran ba su fitar da wata sanarwa ko martani kan waɗannan rahotanni da zarge-zargen ba. Sai dai a baya, hukumomin Amurka sun taɓa ikirarin cewa sun dakile wasu yunƙurin da ake zargin Iran ta yi na kashe Donald Trump.

0 $type={blogger}: