Aƙalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar gobarar daji da ta tashi a yankin Andalusia da ke kudancin ƙasar Sifaniya, lamarin da ya zama gobarar da ta fi kashe mutane a tarihin yankin.
Gobarar ta fara ne a ranar Alhamis kusa da garin Los Gallardos da ke lardin Almeria, kafin iska mai ƙarfi ta bazata zuwa garin Bedar. Mahukunta sun ce an samu wasu daga cikin waɗanda suka mutu a cikin motocinsu yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga gobarar.
Jami'ai sun bayyana cewa har yanzu mutane 19 ba a gano inda suke ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da bincike. Haka kuma, mutane shida sun jikkata, ciki har da wata mata da ta samu munanan ƙonewa da kuma wani da ya shaƙi hayaƙi.
An kwashe kusan mutane 50 daga gidajensu zuwa cibiyar ba da mafaka domin kare lafiyarsu.
Fiye da ma'aikatan ceto 300, ciki har da sojojin rundunar ba da agajin gaggawa ta Sifaniya, na ci gaba da kokarin kashe gobarar.
Haka kuma, an rufe manyan tituna biyu saboda hayaƙi mai yawa.
Ana ci gaba da binciken musabbabin gobarar, duk da cewa rahotannin farko sun nuna cewa wani layin wutar lantarki da ya faɗi na iya zama sanadin tashin gobarar.
Firaministan Sifaniya, Pedro Sánchez, ya bayyana alhininsa kan wannan ibtila'i, tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da kuma yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Lamarin na zuwa ne yayin da tsananin zafi ke ci gaba da addabar sassa da dama na Turai, abin da ke ƙara haɗarin barkewar gobarar daji a faɗin nahiyar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment