Kotun Majistare mai lamba ta 2 da ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Auwal Yusuf Sulaiman ta fara sauraron shari'ar wata matashiya mai suna Fatima Abdullahi (Sele), mai kimanin shekaru 20, wadda gwamnatin jihar Kano ke tuhuma da laifin kashe saurayinta, Ismail Sidi (Buzu).
Rahoton binciken 'yan sanda ya nuna cewa, rikici ya barke tsakanin Fatima da marigayin, inda ake zargin ta bugi Ismail da wani abu a kansa, lamarin da ya janyo masa mummunan rauni tare da zubar jini.
Haka kuma, ana zargin Fatima da kunna wuta a gidanta domin ɓoye shaidun da za su taimaka wajen binciken lamarin.
A zaman kotun na farko, bayan an karanta mata tuhume-tuhumen, Fatima ta musanta aikata laifukan da ake zarginta da su.
Lauyan gwamnati, Barrista Muhammad Aliyu Umar, ya buƙaci kotun ta ba su lokaci domin ci gaba da gabatar da shari'ar.
Sai dai lauyan Fatima ya roƙi kotun da ta ba ta beli saboda halin rashin lafiyar da take ciki, yana mai cewa ta samu raunukan ƙonewa a hannaye, ƙafafu da fuska, kuma tana buƙatar kulawar likita. Ya kafa hujja da sashe na 35 da na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
A nasa martanin, lauyan gwamnati ya bayyana cewa kotun ba ta da ikon bayar da beli a irin wannan shari'a, yana mai cewa akwai ƙwararrun likitoci a gidan gyaran hali da za su kula da ita.
Daga ƙarshe, kotun ta ɗage sauraron shari'ar zuwa 20 ga Yuli, 2026, domin yin nazari kan batun, tare da umartar a ci gaba da tsare Fatima tare da tabbatar da cewa ta samu kulawar likita.

0 $type={blogger}:
Post a Comment