Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki kan wuraren sojin Amurka da ke kasashe biyar na yankin Gulf, tare da sanar da rufe Mashigar Hormuz bayan sabon jerin hare-haren sama da Amurka ta kai, lamarin da ya kara tsananta rikicin da ke gudana.
Mahukuntan Iran sun ce hare-haren sun shafi Bahrain da Kuwait da Qatar da Oman da Jordan, inda suka zargi kasashen da bayar da goyon baya ga ayyukan sojin Amurka ta hanyar karbar sansanoninta da kuma ba ta damar amfani da sararin samaniyarsu.
Wannan sabon rikicin ya biyo bayan hare-haren sama karo na uku da Amurka ta kai cikin mako guda a Iran, inda ta kai farmaki kan cibiyoyin makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki da wuraren hango makamai na Iran. Rundunar CENTCOM ta Amurka ta ce hare-haren na da nufin rage karfin sojin Iran bayan hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa masu zirga-zirga a Mashigar Hormuz.
Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa matakin da kasarsa ta dauka martani ne ga abin da Iran ta kira karya yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da aka cimma tsakanin kasashen biyu a watan da ya gabata.
Rundunar IRGC ta Iran ta yi ikirarin kai hare-hare kan wuraren sojin Amurka da dama, ciki har da sansanin Al Udeid da ke Qatar da sansanonin soja a Jordan, da wasu wuraren sojin Amurka a Kuwait da Bahrain da Oman.
Qatar ta tabbatar da cewa tsarin kariyarta na sama ya dakile wasu makamai masu linzami, yayin da jami'ai suka ce mutane uku sun jikkata sakamakon tarkacen makaman da aka tarwatsa.
Kuwait da Bahrain ma sun ce sun dakile hare-haren ta sama tare da daukar matakan tsaro na gaggawa.
Iran ta kuma sanar da rufe Mashigar Hormuz, tana mai cewa za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai abin da ta kira katsalandan na Amurka a yankin ya kare. Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai da iskar gas a duniya.
Kasashen Gulf da dama, ciki har da Oman da Qatar, sun yi Allah wadai da hare-haren, suna masu bayyana su a matsayin keta hurumin kasashensu tare da gargadin cewa rikicin na iya kara dagula zaman lafiya da tsaron yankin.
Sabbin hare-haren sun kara tayar da fargabar fadada rikicin zuwa matakin yaki mai girma a yankin, yayin da kokarin diflomasiyya na samar da zaman lafiya ke fuskantar babban kalubale..

0 $type={blogger}:
Post a Comment