Sabbin Hare-Hare a jihohin Benue da Plateau Sun Yi Sanadin Mutuwar Mutane 27.

Sabbin Hare-Hare a jihohin Benue da Plateau Sun Yi Sanadin Mutuwar Mutane 27.

Akalla mutane 27 ne suka rasa rayukansu a wasu sabbin hare-hare da aka kai kan al'ummomi a jihohin Benue da Plateau, lamarin da ya sake tayar da hankalin jama'a tare da ƙara kira ga gwamnati da jami'an tsaro su ɗauki matakan gaggawa.

A jihar Benue, mutane 18 ne suka mutu a hare-haren da aka kai kauyukan Akpachi da Otukpo-Nobi da ke karamar hukumar Otukpo. Harin ya fara ne a ranar Juma'a inda aka kashe manoma biyu a gonakinsu, kafin wasu maharan su sake kai farmaki da sanyin safiyar Lahadi, inda suka kashe karin mutane 16 tare da jikkata wasu da dama.

Bayan harin, matasa sun gudanar da zanga-zanga a garin Otukpo, inda suka yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa domin kawo karshen hare-haren da ake yawan kai wa al'ummomin yankin.

Shugaban karamar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana kwashe wadanda suka tsira zuwa wurare masu aminci, tare da bayar da kulawar lafiya ga wadanda suka jikkata, da kuma kara tsaurara matakan tsaro.

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi Allah wadai da hare-haren, yana mai bayyana su a matsayin muggan ayyuka. Ya umarci jami'an tsaro su kara sa ido, su bi sawun maharan tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kuliya.

A jihar Plateau kuwa, wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyukan Kum da Wereng-Camp da ke karamar hukumar Riyom a daren Asabar. Mutane tara daga iyali guda, ciki har da jariri mai watanni biyu, sun rasa rayukansu, yayin da shugaban kauyen ya samu munanan raunuka.

Mazauna yankin sun ce maharan sun shafe fiye da awa guda suna kai hari, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa zuwa dazuka domin tsira da rayukansu. Al'ummomin yankin sun bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Plateau su kara inganta tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

0 $type={blogger}: