Harin Israi'la a kudancin Lebanon yayi sanadin Mutuwar mutum ɗaya, tare da jikkata wasu da dama.

Harin Israi'la a kudancin Lebanon yayi sanadin Mutuwar mutum ɗaya, tare da jikkata wasu da dama.

Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon jerin hare-haren jiragen sama marasa matuƙi na Isra'ila da suka kai hari a yankuna daban-daban na kudancin Lebanon.

Rahotanni sun ce hari mafi muni ya auka kan wani mai babur a hanyar Al-Doha da ke garin Kfarrumman a gundumar Nabatieh, inda mutum ɗaya ya rasa ransa. Wani hari daban da aka kai kan mota a yankin ya jikkata wani mutum mai tsanani, wanda aka garzaya da shi asibiti a birnin Sidon domin samun kulawa.

Tun da farko, wasu mutum biyu sun jikkata bayan wani jirgin sama maras matuƙi ya kai hari kan wata mota da ke tattara shara tsakanin garuruwan Shoukin da Kfar Dajjal.

An kuma kai hare-hare a yankunan Nabatieh al-Fawqa da Al-Hariq kusa da ƙauyen Kfar Tibnit, amma ba a tabbatar da samun asarar rayuka ko jikkata ba.

A gefe guda, sojojin Isra'ila sun gudanar da rushe-rushe a garin Khiam da ke kan iyaka, inda aka rika jin ƙarar fashe-fashe a cikin dare.

Wadannan hare-hare na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Lebanon da Isra'ila ƙarƙashin shiga tsakani na Amurka a ranar 26 ga Yuni, wadda ke da nufin rage tashin hankali da kuma janye dakarun Isra'ila daga kudancin Lebanon.

Mahukuntan Lebanon sun ce rikicin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 4,300, ya jikkata sama da mutum 12,200, tare da raba fiye da mutum miliyan ɗaya da muhallansu tun bayan ƙaruwar rikicin.

0 $type={blogger}: