Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargaɗin cewa ƙasar Amurka za ta kai mummunan hari kan Iran idan ta yi yunkurin kashe shi ko kuma ta yi nasarar aiwatar da hakan.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce rundunar sojin Amurka ta shirya tsaf domin mayar da martani, yana mai cewa an tanadi makamai masu linzami da dama domin kai farmaki kan Iran idan aka kai masa hari.
Ya ce an riga an bai wa sojojin umarni, yana mai jaddada cewa Amurka za ta lalata muhimman wurare a Iran idan gwamnatin Iran ta aiwatar da duk wani shiri na kashe shugaban Amurka.
Sai dai Iran ta musanta zarge-zargen Trump, tana mai cewa ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma da Amurka.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya zargi Amurka da karya wasu sassan yarjejeniyar ta hanyar sake kakaba takunkumi da ɗaukar wasu matakai da ke kawo cikas ga yarjejeniyar.
Sabbin kalaman sun ƙara tsananta rikicin diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu duk da ƙoƙarin da ƙasashe masu shiga tsakani kamar Qatar da Oman ke yi na dawo da tattaunawa da tabbatar da zaman lafiya.
Har ila yau, rikicin ya ƙara ɗaukar hankali kan mashigar ruwa ta Hormuz, wacce ke da matuƙar muhimmanci ga safarar man fetur a duniya, yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da musayar zarge-zarge kan hare-hare da takunkuman tattalin arziki.
Duk da ci gaba da tattaunawa ta hannun masu shiga tsakani, bangarorin biyu na ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai, lamarin da ke sanya makomar zaman lafiyar yankin cikin rashin tabbas.

0 $type={blogger}:
Post a Comment