Masu kashe gobara a ƙasar Spain na ci gaba da fafatawa da wata babbar gobarar daji da ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 12 a yankin Almería da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Gobarar ta tashi ne kusa da ƙauyen Bedar, inda ta bazu cikin gaggawa zuwa yankin Los Gallardos, tare da ƙone fiye da hekta 6,600 na fili. Hukumomi sun ce har yanzu ana neman wasu mutane 23 da suka ɓace, lamarin da ke ƙara fargabar cewa adadin mamatan na iya ƙaruwa.
Daga cikin waɗanda suka mutu akwai mutane huɗu da ake kyautata zaton 'yan Birtaniya ne, bayan an gano gawawwakinsu a cikin wata mota da gobara ta ƙone ƙurmus. Har yanzu hukumomin Spain ba su bayyana sunayensu ba, yayin da ake ci gaba da binciken musabbabin gobarar.
An tura daruruwan jami'an kashe gobara tare da jiragen sama na musamman domin shawo kan ragowar wutar.
Hukumomi sun ce sauyin yanayi da raguwar iska sun taimaka wajen inganta aikin kashe gobarar bayan kwanaki ana kokarin hana ta ci gaba da yaɗuwa.
Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta bazu cikin matuƙar sauri, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin da masu yawon buɗe ido tserewa daga gidajensu domin tsira.
Gobarar na zuwa ne yayin da tsananin zafi ke addabar kasashen kudancin Turai, inda yanayin zafi ya kai kusan digiri 40 na ma'aunin Celsius.
Kasashen Spain da Faransa da Portugal sun fuskanci gobarar daji mai tsanani a wannan bazarar sakamakon zafi mai tsanani da bushewar ciyayi da kuma iska mai ƙarfi.
Hukumomi na ci gaba da aikin ceto da neman waɗanda suka ɓace, tare da kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa su bi umarnin kwashe mutane domin kare rayukansu.

0 $type={blogger}:
Post a Comment