Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) ta tabbatar da cewa mutane biyar ne, ba takwas ba, suka rasu sakamakon guguwar iska da ruwan sama da ta afkawa ƙaramar hukumar Bichi a makon da ya gabata.
Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Isyaku Kubarachi, ya bayyana cewa an tabbatar da adadin ne bayan jami'an hukumar sun kai ziyara yankin domin tantance asarar rayuka da barnar da ibtila'in ya yi.
Ya ce binciken ya kuma gano yawan gidajen da suka lalace da kadarorin da guguwar ta lalata, kafin a miƙa cikakken rahoto ga Gwamnatin Jihar Kano.
Kubarachi ya ƙara da cewa da zarar gwamnati ta samar da kayan tallafi, za a raba su ga waɗanda bala'in ya shafa.
An ruwaito cewa guguwar, wadda ta afku a ranar 22 ga watan Yuli, ta lalata gidaje da dama tare da jawo asarar dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira a ƙaramar hukumar Bichi.
A halin da ake ciki, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta buƙaci gwamnatin jihar da ta gaggauta kai kayan agaji ga al'ummomin da guguwar ta shafa domin rage musu radadin wannan ibtila'i.
Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da wata bukata ta gaggawa da ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Bichi, Lawan Shehu, ya gabatar yayin zaman majalisar da Kakakin Majalisar, Jibril Falgore, ya jagoranta.

0 $type={blogger}:
Post a Comment