Kotun Kano Ta Yankewa Matashiya Hukuncin Kisa Kan Kashe Mijinta Kwana Tara Bayan Aure.

Kotun Kano Ta Yankewa Matashiya Hukuncin Kisa Kan Kashe Mijinta Kwana Tara Bayan Aure.

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wata matashiya mai shekaru 19, Saudat Jibrin, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same ta da laifin kashe mijinta, Salisu Idris, kwanaki tara kacal bayan daurin aurensu.

Alƙaliyar kotun, Mai Shari'a Maryam Sabo, ta yanke hukuncin ne a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin kisan kai da ake tuhumar wadda ake ƙara da shi ba tare da wata shakka ba.

A cewar alkaliyar, "Na yanke miki hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin kisan kai. Kina da kwanaki 90 da za ki ɗaukaka ƙara."

Tun da farko, lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Mayu, 2025, a unguwar Farawa da ke Kano.

Ya ce da misalin ƙarfe 9:00 na dare, Saudat ta sanya wani abu mai guba a cikin abin shan mijinta na "Zobo", sannan ta yanke masa wuya da wuka, kwanaki tara bayan aurensu.

Masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu biyu domin tabbatar da zargin.

Sai dai Saudat Jibrin, wadda ke zaune a Ƙaramar Hukumar Kumbotso, ta musanta aikata laifin a tsawon shari'ar.

An gurfanar da ita ne bisa tanadin Sashe na 221(a) na Kundin Dokokin Hukunta Laifuka (Penal Code) kan laifin kisan kai.

A nasa bangaren, lauyan da ke kare ta, Abdulfatah Muhammad, ya roƙi kotun da ta yi mata sassauci. 
Ya bayyana cewa ta sauya halinta yayin da take tsare, har ma ta haddace Alƙur'ani Mai Girma.

Ya kuma roƙi kotun ta yi la'akari da cewa ita ce babbar 'ya a gidansu, kuma 'yan uwanta na dogaro da ita.

Duk da wannan roƙo, kotun ta same ta da laifi tare da yanke mata hukuncin kisa, sannan ta sanar da ita cewa tana da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 90.

0 $type={blogger}: