Masu Gadin Daji da DSS Sun Ceto Mutane Tara da Aka Sace, Tare da Kashe 'Yan Bindiga Uku a Jihar Kwara.

Masu Gadin Daji da DSS Sun Ceto Mutane Tara da Aka Sace, Tare da Kashe 'Yan Bindiga Uku a Jihar Kwara.

Masu gadin dajin Jihar Kwara tare da jami'an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da mafarauta da masu sa-kai sun ceto mutane tara da aka yi garkuwa da su, yayin da suka kashe wasu da ake zargin 'yan bindiga uku a wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.

An gudanar da aikin tsaron ne a yankunan Obbo-Aiyegunle, Ejiu-Ora da Osi da ke kan iyakar jihohin Kwara da Ekiti da Kogi, bayan samun bayanan sirri kan motsin masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun ce an sace mutanen ne bayan kasuwar Eju, inda masu garkuwar suka nufi da su ta cikin daji zuwa Jihar Neja kafin jami'an tsaro suka tare su.

Daya daga cikin wadanda aka ceto, Umaru Mu'azu, ya ce shi da dansa ne aka yi garkuwa da su bayan wasu dauke da makamai sun tare su. 
Wani da aka ceto, Ibrahim Danga, ya ce ba su dade a hannun masu garkuwar ba kafin jami'an tsaro suka kawo musu dauki.

Wani jami'in Masu Gadin Dajin Kwara, Owolabi Adebayo, ya bayyana cewa sun kashe 'yan bindiga uku bayan musayar wuta, sannan suka ceto mutane tara.

Ya kuma bukaci gwamnati ta samar wa jami'an tsaro karin kayan aiki kamar rigunan kariya daga harsasai  da na'urorin hangen dare da na'urorin sadarwa da karin alburusai domin kara karfafa yaki da masu aikata laifuka a cikin dazuka.

Babban Jami'in Tsaro na Ƙaramar Hukumar Ekiti, Agbemuko Gabriel, ya yaba da kokarin masu gadin dajin, yana mai cewa gudunmawar da suke bayarwa na da matukar muhimmanci wajen inganta tsaro a yankin.

Haka kuma, jami'an tsaron sun nuna wasu babura da suka kwato daga hannun 'yan bindigar yayin wannan samame.

Wannan nasarar ta zo ne yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da kara kaimi wajen sintiri da share dazuka a kudancin Jihar Kwara domin dakile ayyukan garkuwa da mutane da 'yan bindiga. 
Haka kuma, tana zuwa ne bayan amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kafa sabon sansanin bataliyar Sojojin Najeriya a Omu-Aran domin kara inganta tsaro a jihar.

0 $type={blogger}: