Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da samar da magani da kula da lafiya kyauta ga dukkan tsofaffin ma'aikatan gwamnatin jiha da na kananan hukumomi domin rage musu wahalar samun kulawar lafiya bayan sun yi ritaya.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya ta Gudummawar Jama'a ta Jihar Yobe, Dakta Babagana Tijjani, ne ya bayyana hakan, inda ya ce an fara shigar da tsofaffin ma'aikata kimanin 20,000 cikin shirin a matsayin matakin farko. Ya ce ana gudanar da rajistar a dukkan kananan hukumomi 17 na jihar.
A cewarsa, shirin wani bangare ne na manufofin gwamnatin Gwamna Buni na tallafa wa marasa galihu, inda tsofaffin ma'aikatan za su rika samun cikakkiyar kulawar lafiya ba tare da biyan ko sisin kwabo ba.
Dakta Tijjani ya kuma bayyana cewa cikin shekaru bakwai da suka gabata, gwamnatin jihar ta shigar da ma'aikatan gwamnati sama da 45,000 cikin tsarin inshorar lafiya na ma'aikata. Ya ce ma'aikaci na bayar da kashi 1.75 cikin 100 na albashinsa, yayin da gwamnatin jihar ke kara biyan kashi 3.25 cikin 100.
Ya kara da cewa duk da cewa an yi wa ma'aikata kusan 45,000 rajista, adadin masu anfani da ke cikin tsarin a halin yanzu ya kai kusan 35,000, sakamakon wasu sun yi ritaya, wasu sun rasu, yayin da wasu kuma suka bar aikin gwamnati.
Sai dai ya amince cewa karuwar yawan masu cin gajiyar shirin na jefa kalubale ga cibiyoyin lafiya, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na daukar matakan inganta kayan aiki da ayyukan kiwon lafiya domin biyan bukatun al'umma.

0 $type={blogger}:
Post a Comment