Dakarun Sojin Najeriya Sun Ceto Shugaban Kwalejin Fasaha da Wasu Mutum 22, a jihar Zamfara.

Dakarun Sojin Najeriya Sun Ceto Shugaban Kwalejin Fasaha da Wasu Mutum 22, a jihar Zamfara.

Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma (Operation Fansan Yamma) sun ceto Shugaban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda, Dakta Aminu Yusuf, tare da wasu mutum 22 da aka yi yunkurin sacewa a hare-hare daban-daban da aka kai a Jihar Zamfara.

A cewar rundunar sojin, an gudanar da waɗannan samame ne bayan samun kiran gaggawa kan hare-haren da ’yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Kaura Namoda.

Mai magana da yawun Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce ’yan bindigar sun kai hari gidan Dakta Aminu Yusuf da ke unguwar Tsohon Tasha, inda suka kashe jami’in tsaronsa guda tare da jikkata wani mazaunin yankin kafin su yi yunkurin sace shi da iyalansa.

Ya ce dakarun sun isa cikin gaggawa, suka yi artabu da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin shugaban kwalejin da iyalansa, waɗanda aka ceto ba tare da sun ji rauni ba.

A wani samame na daban, dakarun sun dakile wani yunkurin satar mutane a ƙauyen Tungan Dorawa da ke Barkeji, inda suka bi sahun maharan duk da wahalar dajin, suka fatattake su tare da ceto mutanen da aka kai wa hari.

Haka kuma, dakarun sun ceto fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Azaria, tare da wasu fararen hula 21 bayan ’yan bindiga sun yi yunkurin sace su daga gidajensu.

A yayin gudanar da waɗannan ayyuka, jami’an tsaron sun kama Falalu Yusuf mai shekaru 45, wanda ake zargin yana ba ’yan bindiga bayanan sirri da goyon baya. An miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike.

Operation Fansan Yamma ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma, tare da tabbatar wa al’umma cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da inganta tsaro a yankin.

0 $type={blogger}: