Hare-haren Isra'ila Sun Hallaka wani Bafalasdine, tare da Rushe Masallaci a Zirin Gaza.

Hare-haren Isra'ila Sun Hallaka wani Bafalasdine, tare da Rushe Masallaci a Zirin Gaza.

Akalla Bafalasdine guda ɗaya ne ya rasa ransa, yayin da fiye da mutum 12 suka jikkata sakamakon hare-haren sama da Isra'ila ta kai a sassa daban-daban na Zirin Gaza.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai harin ne kan Masallacin Al-Muttaqin da ke birnin Gaza, lamarin da ya lalata masallacin tare da tantunan da daruruwan mutane da suka rasa matsugunansu ke zaune a cikinsu. Rahotanni sun ce an ba mazauna yankin ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai su fice kafin harin ya auku.

A wani hari dabam da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat, mutum guda ya mutu yayin da sama da mutum 20 suka jikkata bayan an kai hari kan wata kasuwa mai cunkoso, kamar yadda jami'an lafiya suka bayyana.

Hare-haren na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta shiga tsakani wajen samar da ita tun watan Oktoban bara. 
A baya-bayan nan, gwamnatin Isra'ila ta amince da wani shiri da zai bai wa rundunar kasa da kasa damar fara shiga Gaza a ƙarƙashin tsarin yarjejeniyar.

A lokaci guda kuma, rikici ya ci gaba a Gabar Yamma da Kogin Jordan, inda rahotanni suka ce wasu mazauna Isra'ila sun banka wa wani gidan Falasdinawa wuta a kusa da Bethlehem, lamarin da ya tilasta wa iyalai takwas tserewa daga gidajensu.

Haka kuma, jami'an Falasdinawa sun ce Isra'ila ta bayar da umarnin ƙwace kimanin dunum 200 na ƙasa a lardin Jenin domin faɗaɗa hanyoyin soji da sabbin matsugunan yahudawa.

Ci gaba da waɗannan hare-hare da tashe-tashen hankula na ƙara dagula halin tsaro a yankunan Falasdinawa, yayin da mazauna yankunan ke ci gaba da fargabar sake barkewar sabbin hare-hare.

0 $type={blogger}: