Wani makiyayi mai shekaru 41, Musa Lawal, ya fadi sumamme bayan shanunsa guda 42 sun mutu a ƙauyen Koroko da ke Ƙaramar Hukumar Kwali a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ma'ajin ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) shiryar Abuja, Yahuza Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce abin ya faru ne a ranar Talata bayan 'ya'yan makiyayin biyu sun fita kiwon shanun.
A cewarsa, daga baya an gano shanun sun mutu a wurare daban-daban a cikin daji bayan sun yi kiwo. Ana zargin cewa sun ci ciyawar da aka fesa wa sinadarai masu guba, sai dai har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar ba.
Bayan da Musa Lawal ya samu labarin abin da ya faru, ya garzaya wurin, amma ya fadi sumamme saboda tsananin firgici da takaicin asarar shanunsa. An kai shi Asibitin Gwamnati na Kwali, inda aka ba shi kulawa kafin daga bisani aka sallame shi bayan ya farfaɗo.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kwali, Hon. Nuhu Daniel Kwali, tare da shugabannin al'ummar Fulani, sun kai ziyara ga iyalan makiyayin domin jajanta musu.
Hukumar ƙaramar hukumar ta umarci jami'an tsaro, ciki har da Hukumar Tsaro ta DSS, su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin mutuwar shanun.
Haka kuma, hukumomin sun bayyana cewa suna duba hanyoyin tallafa wa makiyayin tare da ɗaukar matakan da za su hana barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin.
Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Source: Dailytrust

0 $type={blogger}:
Post a Comment