Wata mata mai suna Nana Batula tare da 'ya'yanta biyu sun samu 'yanci bayan sun shafe kusan wata guda a hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.
An sace su ne a ranar 30 ga watan Mayu, 2026, lokacin da wasu 'yan bindiga masu ɗauke da makamai suka kai hari gidan iyalansu da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe. A yayin harin, maharan sun kashe mijinta, Sagir Umar, kafin su tafi da ita da 'ya'yanta.
Wata majiya ta kusa da iyalan ta tabbatar da sakin su, tare da bayyana godiya ga Allah bisa dawowarsu cikin ƙoshin lafiya.
Majiyar ta ƙara da cewa a halin yanzu Nana Batula da 'ya'yanta na samun kulawar likitoci da kuma taimakon masana kan lafiyar ƙwaƙwalwa domin murmurewa daga halin da suka shiga.

0 $type={blogger}:
Post a Comment