An tsare wani ɗan ƙasar Gambiya a gidan yari bayan ya ji wa matarsa rauni a ido saboda abincin da ta dafa mashi.

An tsare wani ɗan ƙasar Gambiya a gidan yari bayan ya ji wa matarsa rauni a ido saboda abincin da ta dafa mashi.

An tsare wani ɗan ƙasar Gambiya mai suna Lamin Badjie a gidan yari bayan ya amsa laifin dukan matarsa tare da raunata mata ido ɗaya sakamakon takaddama kan abincin da ta ba shi.

Lamarin ya faru ne a makon da ya gabata a garin Foni Mandina, inda aka ce Badjie ya fusata bayan matarsa Fatou Sanneh ta kawo masa abincin dare wanda bashi yake so ba.

Bayan kama shi, an kai shi Brikama Police Station, sannan aka gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare ta Brikama ranar Alhamis, 2 ga Yulin 2026. A kotu, Badjie ya amsa laifin dukan da ya jawo wa matarsa mummunan rauni.

Kotun ta ci tarar sa Dalasi 100,000, sannan ta umarce shi da ya biya matarsa Dalasi 100,000 a matsayin diyya. Haka kuma kotun ta ba da umarnin a tsare shi a Gidan Yarin Mile 2.

A cewar Fatou Sanneh, rikicin ya fara ne bayan mijinta ya dawo gida ya nemi a kawo masa abincin dare.

Ta ce ta ba shi nyankatang tare da benachin, amma yana ci ya ci gaba da korafin cewa ba ya son abincin. Ta tambaye shi ko yana son nyankatang ɗin kaɗai, amma ya ci gaba da korafi.

Fatou ta ce daga nan mijin nata ya umarce ta ta kawo masa ruwa. Yayin da take zuwa ɗauko ruwan, ya tofa mata yawu. 
Bayan ta dawo da ruwan kuma tana tafiya, sai ya bi ta, ya jefa kwanon a gabanta sannan ya fara dukanta. Wata gogonsa ta shiga tsakani ta raba su.

Ta ƙara da cewa bayan ta faɗa masa cewa "namijin da yake dukan matarsa ba ya daɗewa da rai", sai ya ƙara fusata, ya sake kai mata hari har ya ji mata mummunan rauni a ido.

An fara kai Fatou asibitin Kanilai, daga bisani aka mayar da ita babban asibitin Bwiam, inda ta kwana tana karɓar magani.

Ma'auratan na da 'ya'ya biyu tare.

0 $type={blogger}: