Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun fara aiwatar da matakin ficewarsu daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), kamar yadda kotun ta tabbatar.
Kasashen uku masu mulkin soja sun sanar da ICC tun a watan Satumban 2025 cewa suna shirin ficewa daga kotun. Bisa dokokin Yarjejeniyar Rome (Rome Statute), ficewar za ta fara aiki ne bayan cikar shekara guda.
Burkina Faso da Mali da Nijar, wadanda suka kafa Kungiyar Kawancen Kasashen Sahel (Alliance of Sahel States - AES), sun kara nesanta kansu da kasashen Yamma, musamman Faransa, tare da kara karfafa hadin gwiwar tsaro da Rasha.
A cikin sanarwar da suka fitar, kasashen ukun sun zargi ICC da kasancewa wata "kayan aikin danniya na mulkin mallaka ta sabuwar siga," suna masu cewa kotun tana nuna wariya ga kasashen Afirka.
Kotun ICC mai hedikwata a birnin Hague na kasar Netherlands tana gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata kisan kiyashi da laifukan cin zarafin bil'adama da laifukan yaki da kuma laifin tayar da hari, idan kotunan kasashensu ba su iya ko ba su son gurfanar da su.
Sai dai ICC ta bayyana damuwarta kan matakin, tana mai gargadin cewa ficewar kasashen uku na iya raunana kokarin kasa da kasa na tabbatar da adalci da kuma kawo karshen rashin hukunta masu aikata manyan laifuka.
A halin yanzu, ICC na da kasashe mambobi 125, duk da cewa manyan kasashe irin su China da Indiya da Rasha da Amurka da Isra'ila ba sa cikin mambobinta.

0 $type={blogger}:
Post a Comment