Ƙarin Wasu 'Yan Najeriya 268 Sun Dawo Daga Afirka ta Kudu Yayin da Ake Ci Gaba da Kwashe 'Yan Kasar.

Ƙarin Wasu 'Yan Najeriya 268 Sun Dawo Daga Afirka ta Kudu Yayin da Ake Ci Gaba da Kwashe 'Yan Kasar.

Wasu ƙarin 'yan Najeriya 268 da aka kwaso daga Afirka ta Kudu sun iso Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, yayin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da dawo da 'yan kasar da rikicin kyamar baki ya shafa.

Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana cewa jirgin Air Peace da gwamnatin tarayya ta dauki nauyinsa ne ya dauko mutanen daga Johannesburg zuwa Legas.

Ta ce Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarnin a ci gaba da aikin kwaso 'yan Najeriya daga Afirka ta Kudu, duk da cewa wa'adin ranar 30 ga Yuni, 2026 da wasu kungiyoyin masu adawa da bakin haure suka sanya ya wuce.

A cewarta, jirage uku da suka gabata sun riga sun dawo da kusan 'yan Najeriya 600, kuma gwamnati za ta ci gaba da kwaso duk wadanda suka yi rajista da kuma kammala tantancewar da ake bukata.

Ministar ta jaddada cewa kare rayuka da muradun 'yan Najeriya da ke kasashen waje na daga cikin manyan manufofin gwamnatin tarayya.

Wannan na zuwa ne yayin da zanga-zangar kin bakin haure ke ci gaba da tsananta a Afirka ta Kudu, inda masu zanga-zangar ke zargin bakin haure marasa takardu da haddasa rashin aikin yi da kuma kara wa ayyukan gwamnati nauyi.

Rahotanni sun ce akalla mutane hudu sun rasa rayukansu sakamakon rikicin, lamarin da ya sa kasashe da dama na Afirka, ciki har da Najeriya da Ghana da Zimbabwe da Malawi da Mozambique, suka fara dawo da 'yan kasarsu bisa radin kansu.

Gwamnatin Najeriya ta kuma bayyana cewa za ta tattauna da gwamnatin Afirka ta Kudu kan batun diyya ga 'yan Najeriya da suka bar kasuwanci da kadarorinsu sakamakon rikicin.

0 $type={blogger}: