An Gudanar da Jana'izar Mutane 10 da suka Mutu a Harin Bam da Aka Kai Wani Gidan Shan Shayi a Damascus.

An Gudanar da Jana'izar Mutane 10 da suka Mutu a Harin Bam da Aka Kai Wani Gidan Shan Shayi a Damascus.

An gudanar da jana'izar mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da ya afku a wani gidan shayi da ke birnin Damascus na ƙasar Syria, inda mutane 10 suka mutu, ciki har da lauyoyi shida.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a gidan Shan shayin Al-Mushairiya da ke yankin Al-Hijaz, kusa da Fadar Shari'a, inda kuma mutane 22 suka jikkata. Gidan shayin ya kasance wurin da lauyoyi da ma'aikatan kotu ke yawan taruwa.

Kungiyar Lauyoyin Syria ta tabbatar da mutuwar lauyoyi shida daga cikin mambobinta, tana mai bayyana cewa sun rasa rayukansu ne yayin gudanar da aikinsu. Rahotannin cikin gida sun bayyana sunayensu da Muhannad Khalaf, Zuhair Askar, Hossam al-Safadi, Mahmoud al-Shamali, Muhammad Ali al-Shihab da Eid Muhammad Awad.

Mahukuntan Syria sun ce an dasa bam ne a cikin gidan shayin kafin daga bisani aka tayar da shi. Sun musanta jita-jitar cewa dan kunar bakin wake ne ya kai harin, tare da yin alkawarin kamo wadanda suka shirya harin. Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Kasashe da dama da suka hada da Turkiyya, Iraki, Masar, Qatar da Jordan, tare da Tarayyar Turai, sun yi Allah wadai da harin, suna masu jajanta wa iyalan wadanda suka rasu tare da bayyana goyon bayansu ga Syria.

Ana kallon wannan hari a matsayin daya daga cikin manyan hare-haren tsaro da suka afku a Damascus tun bayan kafa sabuwar gwamnatin Syria bayan faduwar tsohuwar gwamnatin kasar a watan Disambar 2024.

0 $type={blogger}: