Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa za ta cire Siriya daga jerin kasashen da take zargi da daukar nauyin ta'addanci, matakin da ake ganin zai bude sabon babi a dangantakar kasashen biyu tare da gwamnatin Shugaba Ahmad Al-Sharaa.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya sanar da Majalisar Dokokin kasar cewa matakin zai fara aiki cikin kwanaki 45, idan har 'yan majalisar ba su hana shi ba.
Sanarwar ta zo ne bayan ganawar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi da Shugaban Siriya Ahmad Al-Sharaa a gefen taron kungiyar NATO da aka gudanar a Turkiyya. Trump ya yabawa Al-Sharaa kan kokarinsa na hada kan Siriya bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-Assad a shekarar 2024.
Rubio ya bayyana cewa cire Siriya daga jerin kasashe masu daukar nauyin ta'addanci tare da sassauta takunkuman da aka kakaba mata zai ba kasar damar jawo hannun jari daga kasashen duniya da farfado da tattalin arzikinta da kuma sake gina kasar bayan shekaru na yaki.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Siriya ta yi maraba da matakin, tana mai cewa hakan ya kawo karshen wani mummunan babi da ya fara tun shekarar 1979 lokacin da aka saka kasar cikin wannan jeri.
Jami'an Amurka sun ce matakin ya biyo bayan tabbacin da gwamnatin Siriya ta bayar cewa ba za ta goyi bayan ayyukan ta'addanci na kasa da kasa ba a nan gaba.
Da zarar matakin ya fara aiki, kasashe uku kacal za su rage a jerin Amurka na masu daukar nauyin ta'addanci, wato Iran da Koriya ta Arewa da kuma Cuba.
Ana sa ran wannan sauyi zai saukaka wa kamfanonin kasashen duniya zuba jari a Siriya yayin da kasar ke kokarin sake farfadowa da gina abin da ya lalace sakamakon shekaru na rikici.

0 $type={blogger}:
Post a Comment