Mayakan ƙungiyar ISWAP shida tare da iyalansu sun miƙa wuya ga dakarun Operation Hadin Kai a Ƙaramar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno.
A cewar rundunar sojin, mutanen sun tsere daga maɓoyar 'yan ta'adda da ke Guduf Bubayagwa da Chikide a tsaunukan Mandara kafin su miƙa kansu ga dakarun Bataliya ta 192.
Mukaddashin Jami'in Yaɗa Labarai na Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Mohammed Goni, ya ce wannan na daga cikin nasarorin da rundunar ta samu a baya-bayan nan ta hanyar hare-haren da suka dogara da bayanan sirri da ayyukan ceto da kuma haɗin gwiwar jami'an tsaro.
A wani samame da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Askira/Uba, sojoji sun kuɓutar da mutane biyu da aka yi garkuwa da su daga wata maɓoyar 'yan ta'adda, sannan suka ƙwato kuɗi har Naira miliyan 1.2 da ake zargin kuɗin ayyukan ta'addanci ne, tare da kayan abinci da sauran kayan tallafi.
Haka kuma, an ƙwato Naira miliyan 1,541,500 da wayoyin salula kirar Tecno guda biyu da wasu kayayyaki daga mayakan ISWAP da suka miƙa wuya tare da iyalansu.
A gefe guda, dakarun da ke Sansanin Soji na Logomani a Ƙaramar Hukumar Ngala sun dakile wani hari da mayakan ISWAP suka kai. Ko da yake maharan sun samu shiga wani ɓangare na sansanin, sojojin sun sake haɗa ƙarfi tare da fatattakar su bayan sun yi musu mummunar asara. Sai dai soja guda ɗaya ya rasa ransa yayin fafatawar, yayin da motocin yaƙi guda biyu da wasu kayan aikin soja suka lalace.
Har ila yau, dakarun sun kama wasu da ake zargi da safarar kayan tallafi ga 'yan ta'adda a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda aka ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya, alburusai, kuɗi, kayan gini, mota, tayoyin babura, magunguna da sauran kayayyakin da ake zargin an tanade su ne domin tallafa wa 'yan ta'adda.
Operation Hadin Kai ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan 'yan ta'adda da kuma gudanar da ayyukan ceto a Arewa maso Gabas. Rundunar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana ba 'yan ta'adda abinci, man fetur, sufuri ko wata irin gudummawar tallafi, za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban doka.

0 $type={blogger}:
Post a Comment