Akalla Mutane 11 ne Suka Mutu, Yayin da 19 Suka Jikkata Sakamakon Gobarar Gidan Marayu a ƙasar Aljeriya.

Akalla Mutane 11 ne Suka Mutu, Yayin da 19 Suka Jikkata Sakamakon Gobarar Gidan Marayu a ƙasar Aljeriya.

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 19 suka jikkata bayan wata gobara ta tashi a wani gidan marayu da ke unguwar Mohammadia a birnin Algiers, babban birnin ƙasar Aljeriya, da sanyin safiyar Alhamis.

Jami'an agajin gaggawa sun bayyana cewa mutum 10 sun samu raunukan ƙonewa daban-daban, mutum biyu sun fuskanci matsalar numfashi, yayin da mutum bakwai aka ba su kulawa sakamakon firgici.

Masu aikin ceto sun kuma kwashe mutane biyar masu buƙata ta musamman zuwa wuri mai aminci domin kare lafiyarsu.

Hukumomi sun tura manyan motocin kashe gobara 10 da motocin daukar marasa lafiya 16 da manyan motocin ceto biyu masu tsani, da kuma ƙwararrun jami'an ceto domin shawo kan gobarar da kuma taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

Har yanzu jami'an kashe gobara na ci gaba da aikin ceto da bincike kan musabbabin tashin gobarar. Hukumomi sun ce adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata na iya sauyawa yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto.

0 $type={blogger}: