Shugaban Faransa Emmanuel Macron Zai Kai Ziyarar Aiki Najeriya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron Zai Kai Ziyarar Aiki Najeriya.

Jakadan Faransa a Najeriya da ECOWAS, Marc Fonbaustier, ya sanar da cewa Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, zai kai ziyarar aiki ta ƙasa zuwa Najeriya a wannan kaka ta shekarar nan.

Jakadan ya bayyana hakan ne yayin bikin ranar ƙasa ta Faransa da aka gudanar a Abuja, inda ya ce ziyarar za ta ba shugabannin kasashen biyu damar tantance ci gaban dangantakar Najeriya da Faransa tare da tsara sabbin hanyoyin haɗin gwiwa.

Ya ce ziyarar Macron na zuwa ne shekaru biyu bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai irin wannan ziyara zuwa birnin Paris.

Fonbaustier ya jaddada cewa dangantakar Najeriya da Faransa ta ginu ne kan mutunta juna da daidaito da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida, inda kasashen biyu ke aiki tare wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi da kare muhalli da inganta dimokuraɗiyya da bin doka.

Ya kuma bayyana cewa kasashen biyu na ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa a fannin kasuwanci da noma, da samar da abinci, musamman a Arewacin Najeriya da sauran ƙasashen ECOWAS ta hannun Hukumar Raya Faransa (AFD).

A bangaren tsaro, jakadan ya ce Najeriya da Faransa na ci gaba da haɗa kai wajen yaƙi da ta'addanci da kuma ƙarfafa ƙasashen yankin wajen inganta tsaro.

Hakazalika, ya bayyana cewa zaman da Emmanuel Macron ya yi a Najeriya na tsawon watanni shida lokacin yana ɗalibi shekaru fiye da 20 da suka gabata ya taimaka wajen tsara manufofinsa game da nahiyar Afirka.

Ana sa ran ziyarar Macron za ta ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya, tattalin arziki da tsaro tsakanin Najeriya da Faransa.

0 $type={blogger}: