Yawan mutanen da suka rasa ransu sakamakon girgizar kasar Venezuela ya haura mutune 235.

Yawan mutanen da suka rasa ransu sakamakon girgizar kasar Venezuela ya haura mutune 235,

Kungiyoyin ceto na ci gaba da aikin neman mutanen da suka makale a karkashin baraguzan gine-gine bayan wasu manyan girgizar kasa guda biyu sun afku a Venezuela.

Mahukunta sun bayyana cewa akalla mutane 235 ne suka mutu, yayin da fiye da 4,300 suka jikkata. Yankin bakin tekun arewacin kasar, musamman La Guaira, na daga cikin wuraren da lamarin ya fi shafa.

Girgizar kasar ta lalata gine-gine da dama, ciki har da wasu gidaje a babban birnin kasar, Caracas. Ma’aikatan agaji, jami’an tsaro da karnukan bincike na ci gaba da kokarin gano wadanda suka makale a karkashin tarkacen gine-gine.

Ministan Lafiya na Venezuela, Carlos Alvarado, ya ce asibitoci sun cika da marasa lafiya, inda aka kafa cibiyoyin jinya na wucin gadi domin taimakawa wadanda suka ji rauni.

Kasashe daban-daban sun fara tura tallafin gaggawa zuwa Venezuela. Amurka ta sanar da tallafin gaggawa, yayin da Kanada ta yi alkawarin samar da abinci, ruwa mai tsafta, kayan kiwon lafiya da sauran abubuwan taimako.

Kasar Colombia ma ta tura ma’aikatan ceto da kayan aiki domin taimakawa wajen aikin ceto.

Jami’ai sun yi gargadin cewa matsalolin tattalin arziki da raunanan ayyukan gwamnati da Venezuela ke fuskanta na iya kara wahalar da aikin agaji.

Girgizar kasar ta kuma haifar da katsewar wutar lantarki a wasu wurare, amma rahotannin farko sun nuna cewa manyan cibiyoyin mai da iskar gas ba su samu mummunar barna ba.

0 $type={blogger}: