'Yan Bindiga Sun Kona Makaranta a Neja Duk da Sun Karɓi Naira Miliyan 10.

'Yan Bindiga Sun Kona Makaranta a Neja Duk da Sun Karɓi Naira Miliyan 10.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga sun ƙone wata makarantar firamare da ke garin Dekara a ƙaramar hukumar Borgu na jihar Neja, bayan zargin karɓar kuɗin haraji naira miliyan 10 daga al’ummomin yankin.

Mazauna yankin sun ce maharan sun kai hari ranar Laraba, inda suka ƙona makarantar Central Primary School da ke Dekara. An ce ’yan bindigar sun fito ne daga dajin Kainji Lake National Park kafin su shiga garin.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa al’ummomin Dekara sun tara tare suka biya kuɗin da ’yan bindigar suka nema bayan sun yi barazanar kai hari idan ba a biya ba. Sai dai duk da an biya kuɗin, an ce har yanzu sun dawo suka kai hari tare da kona makarantar.

A wani labarin makamancin haka, an kai wasu sabbin hare-hare a ƙauyukan Dnakau, Lanta da Unguwan Kawo da ke ƙaramar hukumar Shiroro. Mazauna sun ce an kashe mutum ɗaya sannan an sace wani.

Har zuwa lokacin kammala rahoton, rundunar ’yan sandan jihar Neja ba ta fitar da sanarwar hukuma kan lamarin ba.

0 $type={blogger}: