Ƙasar Koriya ta Arewa ta gudanar da gwaje-gwajen Manya-Manyan makamai a wani yunkuri na ƙara ƙarfafa ƙarfin sojinta da kuma matsa lamba a kan iyakarta da Koriya ta Kudu.
Kafofin watsa labaran gwamnatin Koriya ta Arewa sun bayyana cewa shugaba Kim Jong Un ya sa ido kan gwajin wasu makamai da suka haɗa da ingantattun na’urorin harba rokoki da makamai masu linzami da kuma manyan bindigogi masu motsi.
Kim Jong Un ya bukaci sojojin ƙasar su kasance cikin shirin kai hari mai tsauri domin tabbatar da cewa abokan gabansu ba za su kuskura su kai musu hari ba.
Koriya ta Arewa ta ce daya daga cikin makaman da aka gwada na ɗauke da wani sabon nau’in kan makami mai linzami da aka ƙera domin lalata muhimman wurare kamar sansanonin soja da tashoshin jiragen ruwa da wuraren samar da wutar lantarki.
Masana harkokin tsaro sun ce sabbin makaman na iya bai wa Koriya ta Arewa damar kai hari ga kusan dukkan yankunan Koriya ta Kudu.
A martaninta, Ma’aikatar Tsaron Koriya ta Kudu ta sanar da shirin faɗaɗa amfani da jirage marasa matuka a rundunarta. Ta ce za ta horar da kusan 500,000 “jaruman jirage marasa matuka” domin amfani da su a fagen daga na zamani.
Koriya ta Kudu ta kuma zargi Koriya ta Arewa da samun taimakon fasaha daga Rasha, yayin da shugaba Lee Jae Myung ya sanar da shirin ƙarfafa masana’antar kera makamai ta ƙasar.
Amurka na da dubban sojoji a Koriya ta Kudu, kuma rikicin yankin ya ƙara tsananta yayin da tattaunawar diflomasiyya tsakanin Washington da Pyongyang ke ci gaba da kasancewa a tsaka mai wuya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment