Hukumomi a ƙasar Kenya sun kama mutane sama da 350 yayin da jama’a suka fito domin tunawa da cikar shekaru biyu da zanga-zangar adawa da gwamnati ta shekarar 2024 da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
’Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Nairobi da wasu sassan kasar yayin da jama’a ke gudanar da taron tunawa da mutanen da suka mutu a zanga-zangar adawa da karin haraji.
Rahotanni sun ce akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu bayan wasu masu zanga-zangar sun shiga harabar majalisar dokokin kasar a shekarar 2024.
Ministan Harkokin Cikin Gida na Kenya, Kipchumba Murkomen, ya bayyana cewa an kama mutane 355 a sassa daban-daban na kasar, inda ya kira wadanda aka kama da "masu aikata laifuka".
’Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa wasu mutane da suka taru cikin lumana a wajen ofishin ’yan sanda da ke Nairobi bayan an kama mutane shida a wajen majalisa yayin da suke ajiye furanni don tunawa da wadanda suka mutu.
Wasu shaguna da wuraren kasuwanci a tsakiyar birnin Nairobi sun kasance a rufe, yayin da jami’an tsaro suka kafa shingaye tare da tura motocin ruwan tarwatsa jama’a domin hana sake faruwar rikicin da ya faru shekaru biyu da suka gabata.
’Yan adawa, iyalan wadanda aka kashe, da wadanda suka tsira daga cin zarafin jami’an tsaro sun halarci taron tunawa da wadanda suka mutu, suna neman a yi musu adalci.
Edith Wanjiku, wadda danta mai shekaru 19, Ibrahim Kamau, ya mutu a zanga-zangar 2024, ta ce an hana iyalan wadanda abin ya shafa zuwa yin addu’a da ajiye furanni.
Ta yi kira ga Shugaban Kenya, William Ruto, da ya tabbatar an hukunta jami’an da ake zargi da kashe masu zanga-zanga tare da bai wa iyalan wadanda suka mutu diyya.
Masu shirya zanga-zangar sun bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan yadda ’yan sanda suka tafiyar da lamarin tare da samar da tabbacin cewa ba za a sake amfani da karfin da ya wuce kima ba.
Shugaba Ruto ya amince cewa an samu wasu lokuta na amfani da karfin da bai dace ba daga jami’an tsaro, sannan ya ware biliyan 2 na kudin Kenya domin taimaka wa wadanda rikicin ya shafa. Sai dai wasu masu fafutuka sun ce kudin bai wadatar ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment