Akalla mutane takwas ne suka rasu, yayin da aka ceto wasu mutane 26 bayan wani bene mai hawa uku ya ruguje a yankin Alakija da ke jihar Legas ranar Alhamis.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ta tabbatar da sabon adadin wadanda abin ya shafa, inda ta ce ginin da ke kan Old Ojo Road kusa da Alakija Bus Stop ya rushe da misalin karfe 11:37 na safe.
Hukumar ta bayyana cewa an gano gawarwaki takwas, ciki har da ta wata jaririya, yayin da aka samu nasarar ceto mutane 26 da ransu.
A halin yanzu ana ci gaba da aikin ceto, inda jami’an agaji ke bincike a karkashin baraguzan ginin domin gano ko akwai sauran wadanda suka makale.
Hukumomi da dama na cikin aikin ceto, ciki har da LASEMA, hukumar kashe gobara ta Legas, hukumar kashe gobara ta tarayya, rundunar ’yan sanda, sojojin ruwa da kungiyar agaji ta Red Cross.
An shawarci jama’a da su nisanci wajen da abin ya faru domin bai wa jami’an ceto damar gudanar da aikinsu cikin sauki.

0 $type={blogger}:
Post a Comment