Harin Bam Ya Kashe Wakilin Gidan Talabijin na Al Arabiya mallakin ƙasar Saudi Arabiya a Gabashin Yemen.

Harin Bam Ya Kashe Wakilin Gidan Talabijin na Al Arabiya mallakin ƙasar Saudi Arabiya a Gabashin Yemen.

Wani wakilin gidan talabijin na Saudi Arabiya, , a Yemen ya mutu bayan wani bam da aka dasa a cikin motarsa ya tashi, kamar yadda gidan talabijin din ya bayyana ranar Alhamis.

Dan jaridar mai suna Mohammed Aydah, wanda kuma ke aiki da tashar , an kashe shi ne a daren Laraba a birnin Mukalla da ke lardin Hadramout na gabashin Yemen.

Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. Al Arabiya ta ce jami’an tsaro sun gargadi Aydah kimanin wata guda da ya wuce cewa akwai barazana ga rayuwarsa.

Shugaban Majalisar Shugabancin Yemen, Rashad al-Alimi, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan kisan, tare da alkawarin hukunta wadanda suka aikata laifin.

Wannan kisan ya faru ne a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikicen siyasa a Yemen tsakanin bangarori masu adawa. Birnin Mukalla ya taba kasancewa wurin arangama tsakanin dakarun da Saudi Arabiya ke goyon baya da kuma masu neman ballewar yankin da Hadaddiyar Daular Larabawa ke mara wa baya.

Kungiyar Southern Transitional Council (STC) ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai cewa harin ya nuna matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a yankin Hadramout.

Yemen na cikin rikici tun shekarar 2014, bayan da mayakan Houthi suka kwace babban birnin kasar, Sanaa, lamarin da ya sa kawancen da Saudi Arabiya ke jagoranta ya shiga yakin. Har yanzu Yemen na cikin kasashen da suka fi hadari a duniya ga ‘yan jarida.

0 $type={blogger}: