Gwamnan Kano Ya Bukaci Jama’a Su Ci Gaba da Bai Wa Tinubu Goyon Baya.

Gwamnan Kano Ya Bukaci Jama’a Su Ci Gaba da Bai Wa Tinubu Goyon Baya.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu goyon baya, yana mai cewa shugaban ƙasar ya cancanci cikakken goyon baya saboda ƙoƙarinsa na ci gaban Kano da Najeriya.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin-Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Kano ranar Laraba.

Gwamna Yusuf ya yi wannan kiran ne yayin da yake miƙa takardar shaidar lashe zaɓe ga sabon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Dawakin Kudu/Warawa, Shu’aibu Rabi’u Nagogo.

Ya ce Jihar Kano na da dalilin tsayawa tare da Tinubu a gaban zaɓen 2027.

Gwamnan ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin gwamnatin Kano da gwamnatin tarayya, yana mai cewa hakan ya haifar da nasarori ta fuskar ayyukan more rayuwa da ci gaba.

Yusuf ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin jagora mai kishin haɗin kan ƙasa da ci gaba, inda ya buƙaci shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki su ci gaba da haɗin kai.

Ya kuma taya Nagogo murnar nasarar da ya samu, yana mai cewa yana da yakinin zai wakilci al’ummarsa yadda ya kamata a Majalisar Wakilai.

Gwamnan ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin tarayya domin inganta rayuwar jama’a.

0 $type={blogger}: