’Yan Bindiga Sun Kashe Limami, Tare da Sace Mata Masu Yawa a Sokoto.

’Yan Bindiga Sun Kashe Limami, Tare da Sace Mata Masu Yawa a Sokoto.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani limamin masallaci tare da yin garkuwa da wasu mata masu yawa a ƙauyen Ƙuda-Ƙuda da ke ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto, arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga ƙauyen ne da sanyin safiyar Alhamis, inda suka yi ta harbe-harbe na tsawon sa’o’i kafin su bindige Imam Audu har lahira tare da kwashe dabbobi da dama.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun rika shiga gidaje suna ɗaukar mutane, inda mafi yawansu mata ne.

Sun kuma koka da rashin samun isasshen taimako daga jami’an tsaro a lokacin harin, suna mai cewa ƙauyen Ƙuda-Ƙuda ya sha fama da hare-hare a cikin ‘yan shekarun nan.

Wani mazaunin yankin ya ce wannan shi ne hari na 11 da aka kai wa ƙauyen, yana mai bayyana damuwa kan yadda al’ummar yankin ke ci gaba da fuskantar barazana duk da roƙon da suka yi na a kawo musu ɗauki.

Har zuwa yanzu ba a samu martani daga rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ko gwamnatin jihar ba.

0 $type={blogger}: