Yarjejeniyar Mayar da Fursunonin Habasha Ta Yi Daidai da Shirin “Renewed Hope” — Gwamnatin Tarayya.

Yarjejeniyar Mayar da Fursunonin Habasha Ta Yi Daidai da Shirin “Renewed Hope” — Gwamnatin Tarayya.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa yarjejeniyar mayar da fursunoni da aka kulla tsakanin Najeriya da Habasha, wadda za ta ba da damar dawo da ’yan Najeriya da ke gidajen yari a can, ta yi daidai da shirin Shugaba Bola Tinubu na “Renewed Hope” da manufar kare ’yan ƙasa a ƙasashen waje.

Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta ce yarjejeniyar wata muhimmiyar nasara ce ta diflomasiyya wadda ta mayar da hankali kan jin daɗin ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.

Ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta ba wa ’yan Najeriya da aka yanke wa hukunci a Habasha damar komawa gida domin kammala hukuncin da aka yanke musu cikin yanayi mafi kyau.

Ministar ta musanta rahotannin da ke cewa akwai fursunonin Najeriya 136 a gidajen yarin Habasha, inda ta ce jerin sunayen da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai ba gaskiya ba ne. Ta ce fursunoni 98 ne kawai ke cikin yarjejeniyar, wadanda ake tsare da su a gidajen yarin Kaliti da Aba Samuel.

A cewarta, da yawa daga cikin fursunonin sun fuskanci matsaloli kamar rashin isasshen kulawar lafiya, ƙarancin abinci, matsalolin samun lauya, matsalar harshe da kuma hana ziyara.

Ta kuma bayyana cewa fursunoni huɗu ’yan Najeriya sun rasu yayin da ƙasashen biyu ke kammala yarjejeniyar.

Odumegwu-Ojukwu ta ƙaryata zargin cewa za a saki fursunonin bayan dawowarsu Najeriya, inda ta ce yarjejeniyar ba ta ba da damar yin afuwa ko sassauci ga wani fursuna ba tare da amincewar ƙasar da ta yanke hukuncin ba.

Ta ƙara da cewa laifi ba shi da kabila ko yanki, domin mutanen da abin ya shafa ’yan Najeriya ne daga sassa daban-daban na ƙasar.

0 $type={blogger}: