An dakatar da tattaunawar Amurka da Iran saboda ci gaba da kai hare-hare lebanon da Isra’ila ke yi.

An dakatar da tattaunawar Amurka da Iran saboda ci gaba da kai hare-hare lebanon da Isra’ila ke yi.

An dakatar da shirin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran da aka shirya yi a Switzerland domin tattauna hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Switzerland ta tabbatar a ranar Juma’a cewa taron da aka shirya gudanarwa a otal ɗin Burgenstock ba zai gudana ba, kuma ba a bayyana sabuwar ranar taron ba.

Rahotanni sun ce Iran ta jinkirta tura tawagarta zuwa Switzerland ne saboda ci gaba da hare-haren sojin Isra’ila a kudancin Lebanon. Hare-haren sun kashe akalla mutane 16, yayin da ƙungiyar Hezbollah ta ce ana gwabza kazamin yaƙi a yankin.

Taron da aka dakatar ya kamata ya haɗa Amurka da Iran da Qatar da Pakistan domin tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyar mai daftari 14 da aka sanya hannu a wannan makon.

Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya shirya tafiya Switzerland domin jagorantar tawagar Amurka, amma daga baya aka soke tafiyar bayan an kasa kammala shirye-shiryen taron.

Isra’ila da Hezbollah ba sa cikin yarjejeniyar Amurka da Iran, amma Iran ta dage cewa dole Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kudancin Lebanon da take iko da su.

Dakatar da tattaunawar ta zo ne yayin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya duk da ƙoƙarin da ake yi na tsagaita bude wuta da komawa kan tattaunawar diflomasiyya.

0 $type={blogger}: