Gwamnatin Jihar Kano ta kammala gyaran tare da samar da kayan aiki a cibiyoyin lafiya a matakin farko (PHCs) guda 320 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar, domin inganta harkokin kiwon lafiya.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar domin bikin Ranar Dimokuradiyya da cika shekaru uku na gwamnatin Gwamna Abba Yusuf.
Ya ce lokacin da gwamnatin ta karbi mulki a shekarar 2023, ta tarar da cibiyoyin lafiya 1,236 cikin mummunan yanayi, amma a cikin shekaru uku ta gyara tare da samar da kayan aiki ga 320 daga cikinsu.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya ta dauki karin ma’aikatan lafiya tare da tura su zuwa cibiyoyin lafiya domin inganta ayyuka.
Ya kara da cewa jihar na shirin daukar karin ma’aikatan lafiya kusan 7,000 da suka hada da ma’aikatan jinya da ungozoma domin karfafa ayyukan kiwon lafiya.
Dakta Yusuf ya ce gwamnati na kara inganta asibitocin sakandare a kananan hukumomi 44, tare da kokarin tabbatar da samun magunguna masu muhimmanci a cibiyoyin lafiya.
Ya kuma bayyana kafa Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Jihar Kano (Kano State Centre for Disease Control) a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin gwamnatin, inda ya ce cibiyar ta kara wa jihar karfin gano da dakile barkewar cututtuka.
Kwamishinan ya ce an kara karfafa shirin rigakafi na yara a fadin jihar domin hana yaduwar cututtuka musamman diphtheria.
Ya bukaci jama’a da su dauki matakan kariya, ciki har da guje wa cunkoson jama’a da wuraren da ba su da iska mai kyau.
Ya kuma bayyana cewa ana gudanar da gwajin cutar tarin fuka (TB) kyauta ga mazauna jihar, ciki har da mata masu juna biyu.

0 $type={blogger}:
Post a Comment