Sojojin Amurka Sun Kashe Mutane Uku a Harin Jirgin Ruwa da Ake Zargi da Safarar Miyagun Kwayoyi a Tekun Pacific na Gabas

Sojojin Amurka Sun Kashe Mutane Uku a Harin Jirgin Ruwa da Ake Zargi da Safarar Miyagun Kwayoyi a Tekun Pacific na Gabas

Sojojin Amurka sun kashe akalla mutane uku bayan sun kai hari kan wani jirgin ruwa a yankin Tekun Pacific na Gabas, wanda suka zarga da safarar miyagun kwayoyi.

Harin, wanda ya faru ranar Alhamis, shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren da Amurka ke kaiwa kan jiragen ruwa da ake zargin suna da alaka da masu safarar miyagun kwayoyi.

Rundunar Sojojin Amurka ta Yankin Kudu ta ce ta gudanar da wani “hari mai kisa” kan jirgin ruwan da take zargin kungiyoyin da aka ayyana a matsayin ‘yan ta’adda ne ke amfani da shi. Ta ce bayanan sirri sun nuna jirgin yana tafiya a hanyoyin da aka sani da safarar kwayoyi kuma yana cikin harkar fataucin miyagun kwayoyi.

Wani bidiyo da aka fitar tare da bayanin ya nuna kamar an harba makami kan jirgin mai gudu, wanda daga baya ya kama da wuta.

Amurka ta ce mutane akalla 211 ne aka kashe a irin wadannan hare-hare da ta kai a Tekun Pacific. Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce gwamnatinsa na daukar mataki ne a matsayin wani bangare na yaki da kungiyoyin masu safarar kwayoyi a kasashen Latin Amurka.

Sai dai masu suka sun kalubalanci sahihancin hare-haren, suna cewa Amurka ba ta bayar da cikakkun hujjojin da ke tabbatar da cewa duk wadanda aka kashe suna da hannu a safarar kwayoyi ba. 
Wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ‘yan siyasa sun zargi Amurka da yiwuwar kashe wasu masunta da ba su da alaka da kungiyoyin kwayoyi.

A ranar Alhamis, sanatocin Amurka sun bukaci Ma’aikatar Tsaro ta kasar ta fitar da cikakken bidiyon da ba a gyara ba na hare-haren.

Harin farko da aka kai a watan Satumba ya jawo cece-kuce bayan sojojin Amurka sun tabbatar da cewa sun sake kai hari karo na biyu bayan harin farko, lamarin da ya kashe wadanda suka tsira. 
Mutane 11 ne suka mutu a wannan lamari, inda masu sukan lamarin suka ce kashe wadanda suka tsira ya sabawa doka.

0 $type={blogger}: