Jonathan David ya zura kwallaye uku a wasan da Ƙasar Kanada Ta lallasa Qatar da ci 6-0 a Gasar Cin Kofin Duniya na 2026.

Jonathan David ya zura kwallaye uku a wasan da Ƙasar Kanada Ta lallasa Qatar da ci 6-0 a Gasar Cin Kofin Duniya na 2026.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kanada ta kafa tarihi a gasar cin kofin duniya bayan ta samu nasarar farko a tarihinta da ci 6-0 a kan Qatar a wasan rukuni na B da aka buga a BC Place da ke Vancouver.

Dan wasan Kanada, Jonathan David, ne ya haskaka a wasan inda ya zura ƙwallaye uku, yayin da Cyle Larin da Nathan Saliba suka ƙara wasu ƙwallayen. Haka kuma, ɗan wasan bayan Qatar, Mohamed Manai, ya ci gida bisa kuskure.

Lamarin ya sauya yanayin wasan bayan ɗan wasan tsakiya na Kanada, Ismael Kone, ya samu mummunan rauni bayan arangama da ɗan wasan Qatar, Assim Madibo, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

An fara ba Madibo katin rawaya, amma bayan nazarin VAR aka sauya shi zuwa jan kati kai tsaye, abin da ya sa Qatar ta ci gaba da wasa da 'yan wasa tara, bayan an kori Homam Ahmed tun a farkon wasan.

Da yawan 'yan wasa a filin wasa, Kanada ta ƙara matsa lamba. Nathan Saliba ya zura ƙwallo ta bugun tazara a minti na 64, sannan ya yi bikin ƙwallon ta hanyar ɗaga rigar Kone domin nuna goyon baya gare shi.

Kanada ta ci gaba da mamaye wasan, kafin Manai ya ci gida, sannan David ya kammala zura kwallon sa ta uku bayan ƙarin lokaci.

David ya zama ɗaya daga cikin 'yan wasa kaɗan da suka ci kwallaye uku a gasar cin kofin duniya ta 2026, kuma shi ne ɗan wasan Kanada na farko da ya ci ƙwallaye fiye da ɗaya a wasa guda na gasar.

Duk da wannan babbar nasara, David ya ce raunin Kone ya rage musu farin cikin nasarar.

Bayan an tashi daga wasan, rikici ya ɓarke tsakanin 'yan wasan ƙungiyoyin biyu, lamarin da ya sa jami'an wasa suka shiga tsakani domin raba su.

Nasarar ta sanya Kanada a matsayi mai ƙarfi na zama ta farko a rukunin B, inda take buƙatar canjaras kawai a wasan ƙarshe da Switzerland.

0 $type={blogger}: