'Yan Sandan Vietnam Sun Ceto Fiye da maguna 400 Daga Kasuwancin Nama Ba Bisa Ka’ida ba

'Yan Sandan Vietnam Sun Ceto Fiye da maguna 400 Daga Kasuwancin Nama Ba Bisa Ka’ida ba

’Yan sandan Vietnam sun ceto fiye da maguna 400 da aka sace, a wani babban samame da aka kai kan wata ƙungiyar masu safarar dabbobi domin sayar da namansu a birnin Ho Chi Minh.

Ƙungiyoyin kare dabbobi sun ce an mayar da fiye da maguna 40 ga masu su bayan aikin ceto, amma wasu daga cikin dabbobin da aka gano sun mutu sakamakon mummunan yanayin da aka tsare su a ciki.

Masu fafutukar kare dabbobi sun bayyana lamarin a matsayin wata shaida da ke nuna girman kasuwancin naman cat a Vietnam.

’Yan sanda sun fara bincike ne bayan samun rahotannin satar dabbobin gida a Ho Chi Minh. Binciken ya kai su ga gano wata ƙungiyar masu safarar naman maguna, inda aka kama mutane tara.

Jami’an tsaro sun gano kejin dabbobi 45 da ke ɗauke da kusan maguna 400 masu rai, sannan aka gano wasu kwantena da ke ɗauke da kusan maguna 80 da suka mutu. A wani wuri kuma an ceto wasu maguna 21 masu rai.

’Yan sanda sun ce waɗanda ake zargi sun amsa cewa sun kwashe shekaru uku suna kamawa da tara magunan a kudancin Vietnam, ciki har da Ho Chi Minh, Tay Ninh da An Giang.

Masu kare dabbobi sun ce miliyoyin karnuka da maguna ne ke fuskantar sacewa a Vietnam, inda ake ɗaukar su daga tituna ko kuma a sace su daga gidajen mutane domin a yanka su don cin nama.

Wani mai aikin sa kai na ƙungiyar jin dadin magunan Vietnam, ya ce iyalai da dama sun zo neman dabbobinsu da suka ɓace, wasu sun samu nasarar gano su, yayin da wasu kuma suka koma gida ba tare da sun same su ba.

Likitocin dabbobi da masu aikin sa kai na ci gaba da kula da dabbobin da aka ceto.

Duk da cewa cin naman karnuka da maguna ya halatta a Vietnam, masu sayarwa dole ne su kasance da takardun izini da ke tabbatar da asalin dabbobin. Wasu garuruwa kamar Hoi An na aiki tare da ƙungiyoyin kare dabbobi na duniya domin rage wannan al’ada.

Jami’an Vietnam sun kuma bayyana cewa suna shirin gyara wasu dokoki domin ƙara kare dabbobin gida da kuma haƙƙin masu su.

0 $type={blogger}: