Akalla manoma biyar ne suka rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a wani wurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Gero na gundumar Gyel, a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana ranar Talata, sa’o’i kaɗan bayan wani hari da aka ruwaito a kusa da "Babbar Cibiyar Nazari kan Manufofi da Tsare-tsaren Dabarun Ƙasa (NIPSS)" da ke Kuru, ita ma a Jos ta Kudu.
Wani mazaunin yankin mai suna Ritiji Dalyop ya ce mutanen da aka kashe suna gudanar da aikin haƙar ma’adinai ne lokacin da maharan suka mamaye wurin tare da buɗe musu wuta ba tare da tare da zabi ba.
“Mutane biyar ne ‘yan bindigar suka harbe suka mutu a wurin,” in ji Dalyop.
Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar Berom Youth Moulders Association (BYM), Rwang Tengwong, shi ma ya tabbatar da harin. Ya bayyana cewa lamarin na daga cikin matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankunan da ke kewaye, yana mai nuna damuwa kan lafiyar mazauna yankin.
Ƙungiyar ta kuma yi nuni da wani hari da ya faru a baya a yankin Kuru kusa da NIPSS, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro uku.
BYM ta buƙaci hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin dakile hare-haren da ke faruwa tare da dawo da zaman lafiya da kwarin gwiwa ga al’ummomin da abin ya shafa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, SP Alabo Alfred, ya ce har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai samu cikakken bayani daga jami’an yankin ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment