Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta gano tare da ware guraben kiwo guda 470 da aka amince da su bisa doka a fadin kasar nan, a wani yunkuri na kawo karshen kiwon dabbobi a bude da yawo da shanu a manyan tituna da birane.
Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Idi Maiha, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Arise News, inda ya yi bayani kan yadda gwamnati ke aiwatar da Tsarin Manufofin Samar da Madara na Kasa da kuma shirinta na inganta harkar kiwo a Najeriya.
Maiha ya ce gwamnati za ta gyara wadannan guraben kiwo tare da mayar da makiyaya cikinsu domin inganta kula da lafiyar dabbobi da sa ido kan cututtuka da kuma bunkasa jinsin dabbobi masu yawan anfani.
Ya bayyana cewa gwamnati na wayar da kan makiyaya su rungumi tsarin zama a wuri guda, yana mai cewa kiwon dabbobi a bude da kuma yin doguwar tafiya da shanu ba su da amfani ga ci gaban harkar kiwo a wannan zamani.
A cewarsa, gwamnati na shirin sanya na’urorin tantancewa a jikin dabbobi, ta yadda idan saniya ta fita daga yankin da aka ware mata za a samu gargadi nan take, wanda zai taimaka wajen gano dabbar ko kuma dawo da ita idan ta bata.
Ministan ya kuma nuna damuwa kan karancin madarar da shanun Najeriya ke samarwa. Ya ce a halin yanzu saniya a Najeriya na samar da tsakanin lita 1.2 zuwa 2 na madara a rana, yayin da a wasu kasashe kamar Kenya shanu ke samar da har lita 30 a rana.
Ya danganta wannan gibin da rashin ingantattun jinsunan dabbobi da matsalolin ciyarwa da kuma rashin ingantaccen tsarin kula da cututtuka.
Maiha ya kara da cewa duk da cewa Najeriya na da kimanin dabbobi masu tauna ciyawa miliyan 270, ciki har da shanu da tumaki da awaki da rakuma, har yanzu kasar ba ta samu ci gaba sosai wajen inganta jinsin dabbobinta ba.
Ya ce gwamnati na mayar da hankali wajen inganta ciyarwa da yaki da cututtuka da kuma bunkasa jinsin dabbobi domin kara yawan samar da madara a gida da rage shigo da ita daga kasashen waje da kuma habaka bangaren kiwo a Najeriya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment