Dan wasan gaba Erling Haaland ya ci kwallaye biyu yayin da Norway ta fara gasar Kofin Duniya ta 2026 da nasara bayan ta doke Iraq da ci 4-1 ranar Talata.
Dan wasan na Manchester City ne ya fara jefa kwallo a ragar Iraq a minti na 29 a birnin Boston, amma Iraq ta dawo da martani ta hannun Aymen Hussein wanda ya rama da kai.
Haaland ya sake bai wa Norway damar nasara kafin a tafi hutun rabin lokaci bayan ya ci gajiyar kuskuren da ‘yan wasan bayan Iraq suka yi, lamarin da ya kai yawan kwallayen da ya ci wa kasarsa zuwa 57 a wasanni 51.
Daga baya Norway ta kara tazarar kwallaye bayan Leo Østigård ya ci ta uku da kai, kafin a samu kwallo ta hudu bayan wani kuskuren dan wasan Iraq da ya zura kwallon a ragar ƙasarsa.
Nasarar ta sanya Norway zama ta daya a rukunin I bisa bambancin kwallaye, inda take da maki uku daidai da Faransa wadda ta doke Senegal da ci 3-1.
Norway za ta kara da Faransa a wasanta na gaba a ranar 22 ga Yuni a birnin New Jersey.
Iraq, wadda ta samu gurbin gasar a matsayin kungiya ta karshe, tana buga gasar Kofin Duniya ne karo na farko tun bayan shekarar 1986.

0 $type={blogger}:
Post a Comment