'Yan sandan Faransa sun kama kusan mutane 20 a birnin Paris ranar Asabar, bayan daruruwan masu zanga-zanga sun gudanar da gangamin adawa da danniya da kuma kisan gilla da suka yi zargin ana yi a ƙasar Iran duk da haramcin da hukumomi suka sanya.
Masu zanga-zangar sun taru a dandalin Place Vauban da ke tsakiyar birnin Paris bayan wasu motocin bas sun isa wurin. Hukumomin Faransa sun hana gudanar da zanga-zangar ne saboda fargabar barkewar rikici tsakanin masu zanga-zangar da masu goyon bayan gwamnatin Iran a daidai lokacin da ake fama da matsanancin yanayi na siyasa a duniya.
Kungiyoyin 'yan Iran da ke zaune a kasashen waje tare da wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama na Faransa da na duniya ne suka shirya zanga-zangar domin nuna damuwa kan yadda suke zargin ana take hakkin dan Adam tare da aiwatar da hukuncin kisa a Iran.
Masu zanga-zangar sun rika rera taken adawa da gwamnatin Iran, tare da daga hotunan mutanen da suka ce hukumomin Iran sun kashe.
Daga bisani 'yan sanda sun tarwatsa taron ta hanyar amfani da sinadarin barkono mai sa hawaye. Masu shirya zanga-zangar sun ce an kama mutane kusan 20 tare da jikkata wasu 12, amma sun dage cewa zanga-zangar ta kasance cikin lumana.
Wata kotun Paris ta amince da haramcin zanga-zangar bayan masu shirya taron sun shigar da kara domin a soke dokar hana taron.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce an kashe sama da mutane 40 ta hanyar hukuncin kisa a Iran tun bayan fara rikicin yankin, inda wasu daga cikin wadanda aka kashe ake alakanta su da zanga-zangar adawa da gwamnati da ta gabata.

0 $type={blogger}:
Post a Comment