Gwamnatin jihar Abia Ta Haramta Zirga-zirgar Okada a Aba da Umuahia da Ohafia Saboda Matsalar Tsaro.

Gwamnatin jihar Abia Ta Haramta Zirga-zirgar Okada a Aba da Umuahia da Ohafia Saboda Matsalar Tsaro.

Gwamnatin Jihar Abia ta amince da haramta aikin babura masu ɗaukar fasinjoji, wato okada, a manyan garuruwan Aba da Umuahia da Ohafia.

Gwamnatin ta bayyana cewa an dauki wannan matakin ne domin inganta tsaro da kare lafiyar jama’a da rage matsalolin cunkoson ababen hawa, da kuma samar da ingantaccen tsarin sufuri a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Abia, Okey Kanu, ya fitar ranar Asabar, ya ce dokar za ta fara aiki daga Litinin, 22 ga watan Yuni, 2026.

Gwamnatin ta umarci dukkan masu sana’ar okada da su dakatar da ayyukansu a wuraren da abin ya shafa kafin ranar fara aiki da dokar.

An kuma umarci jami’an tsaro da hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar da wannan umarni. 
Gwamnatin ta gargadi cewa duk wanda ya karya dokar za a kama shi, sannan a kwace babur din da aka yi amfani da shi bisa doka.

An bukaci mazauna jihar, masu safarar jama’a da shugabannin al’umma da sauran jama’a su ba da hadin kai ga hukumomi domin tabbatar da nasarar aiwatar da wannan mataki.

0 $type={blogger}: