Hukumar dake kula da harkokin magunguna ta Najeriya (PCN) ta rufe gidajen sayar da magunguna guda 724 a Jihar Kwara saboda karya ka’idojin aiki.
Magatakardar hukumar, Ibrahim Ahmed, ne ya bayyana hakan a Ilorin bayan kammala wani aikin bincike da duba wuraren sayar da magunguna na tsawon kwanaki hudu a jihar.
Binciken ya shafi kananan hukumomi 10 da suka hada da Ilorin ta Kudu da Ilorin ta Gabas da Ilorin ta Yamma da Asa da Offa da Ifelodun da Oyun da Moro da Irepodun da Edu.
PCN ta ce ta duba wurare 1,238, ciki har da gidajen sayar da magunguna 167 da shagunan magani masu lasisi 957 da kuma wuraren sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba guda 114.
Daga cikin wuraren da aka duba, an rufe guda 724, ciki har da gidajen magani 68 da shagunan magani masu lasisi 542 da wuraren haramtattun sayar da magunguna 114.
Hukumar ta ce laifukan da aka gano sun hada da aiki ba tare da lasisin PCN ba, rashin kyakkyawan tsarin ajiye magunguna da bai wa mutane damar siyan magungunan da aka sarrafa ba bisa ka’ida ba da horar da dalibai ba tare da tsari ba, da kuma dafa abinci a cikin shagunan magani.
PCN ta gargadi cewa irin wadannan ayyuka na jefa lafiyar jama’a cikin hadari tare da kara yiwuwar amfani da magunguna masu hatsari ta hanyar da ba ta dace ba.
Hukumar ta shawarci jama’a su rika sayen magunguna daga wuraren da aka ba su lasisi kawai domin kauce wa matsalolin rashin samun waraka da jurewar kwayoyin cuta ga magunguna da kuma mace-macen da za a iya kauce wa.
Ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da daukar mataki kan duk wani wurin da ya karya dokokin sayar da magunguna a Najeriya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment