An gudanar da wani bikin aure na musamman a birnin Ibadan na jihar Oyo, inda wasu ‘yan tagwaye maza suka auri ‘yan tagwaye mata a rana guda, lamarin da ya ja hankalin mutane sosai.
‘Yan uwan tagwayen maza, Oguntoye Taiwo Oye da Oguntoye Kehinde Oladele, sun yi aure da ‘yan tagwaye mata da suke da sunaye iri daya da nasu — Taiwo da Kehinde.
Ma’auratan sun wallafa hotunan bikin al’adarsu a shafukan sada zumunta, inda suka nuna godiya ga Allah, iyalai da abokan arziki saboda taimakawa wajen ganin ranar ta kasance mai armashi.
Sun bayyana cewa bikin ya zama sabon mataki na rayuwa mai cike da soyayya, hadin kai da albarka.
Hotunan bikin sun bazu a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka taya su murna tare da bayyana cewa irin wannan lamari ba kasafai yake faruwa ba.
A al’adar Yarbawa, ana sanya wa dan tagwaye na farko suna Taiwo, wanda ke nufin “wanda ya fara dandana duniya,” yayin da na biyu ake kira Kehinde, wato “wanda ya zo bayansa.”

0 $type={blogger}:
Post a Comment