‘Yan Sanda Sun yi arangama da masu Zanga-zangar Adawa da gina Cibiyar Killace Masu fama da cutar Ebola da Amurka ke kokarin samarwa a Kenya

‘Yan Sanda Sun yi arangama da masu Zanga-zangar Adawa da gina Cibiyar Killace Masu fama da cutar Ebola da Amurka ke kokarin samarwa a Kenya

Rikici ya ɓarke ne a garin Nanyuki da ke tsakiyar ƙasar Kenya bayan daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar adawa da Samar da cibiyar killace mutanen da suka kamu da cutar Ebola, wadda Amurka ke shirin kafawa a sansanin sojin sama na Laikipia.

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da motar feshi da ruwa da kuma harbe-harbe domin tarwatsa masu zanga-zangar bayan sun toshe hanyoyi tare da jifan jami’an tsaro da duwatsu.

Masu zanga-zangar sun nuna rashin amincewarsu da shirin kafa cibiyar, suna zargin cewa Amurka na ƙoƙarin mayar da haɗarin kula da mutanen da suka yi mu’amala da masu cutar Ebola zuwa Kenya.

Mutane da dama sun bayyana damuwa cewa Kenya ba ta taɓa samun bullar cutar Ebola ba, don haka bai kamata a kawo waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ko suka yi hulɗa da masu ita cikin ƙasar ba.

An tsara cibiyar ta ƙunshi gadajen killace marasa lafiya guda 50, kuma ma’aikatan Amurka ne za su tafiyar da ita.

Gwamnatin ƙasar ta Kenya ta dage kan aiwatar da shirin Duk da umarnin wata babbar kotun ƙasar na dakatar da aikin na ɗan lokaci da kuma adawar wasu shugabannin yankin, gwamnatin Shugaba William Ruto ta ce za ta ci gaba da aiwatar da shirin.

Gwamnatin ta bayyana cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin Kenya da Amurka ya haɗa da tallafin lafiya da shirye-shiryen tunkarar annoba, inda Amurka ta ware miliyoyin daloli domin ƙarfafa shirin kariya daga Ebola a Kenya.

An kama mutane da dama yayin tarzomar, yayin da hotuna daga wurin suka nuna arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.

Rahotanni sun kuma nuna cewa aƙalla mutum guda ya mutu a yayin rikicin, kodayake hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.

Zanga-zangar ta ƙara fito da rabuwar kai tsakanin jama’a da gwamnati kan yadda za a tunkari barazanar Ebola a yankin Gabashin Afirka.
Yayin da masana kiwon lafiya ke ganin shirye-shiryen kariya suna da muhimmanci wajen hana yaɗuwar cutar, mazauna yankin suna tsoron cewa cibiyar killacewar za ta iya jawo haɗari ga Kenya.

0 $type={blogger}: