Ƙasar Isra’ila ta yi alkawarin ƙara zurfafa haɗin gwiwa da Najeriya a fannin ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaba

Ƙasar Isra’ila ta yi alkawarin ƙara zurfafa haɗin gwiwa da Najeriya a fannin ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaba

Isra’ila ta sanar da shirin ƙarfafa haɗin gwiwarta da Najeriya a muhimman fannoni da suka haɗa da ƙirƙire-ƙirƙire (innovation) da noma sa kiwon lafiya da tsaro da ilimi da horar da ƙwarewa.

Jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin cikar Isra’ila shekaru 78 da kafuwa.

Freeman ya ce wannan faɗaɗa haɗin gwiwa ba taimako ba ne, illa dai saka hannun jari ne a makomar da ƙasashen biyu ke raba, yana mai cewa haɗin gwiwar hazakar matasan Najeriya da fasahar Isra’ila na iya samar da manyan ci gaba na tattalin arziki da zamantakewa.

Ya bayyana cewa akwai shirye-shirye da ke gudana da ke haɗa ‘yan kasuwar Najeriya masu ƙirƙire-ƙirƙire da masu ba su horo daga ƙasashen biyu domin samar da hanyoyin kasuwanci da ayyukan yi.

A cewarsa, kamfanonin Isra’ila sun riga sun fara aiki a fannin noma a Najeriya, kuma ana shirin ƙarin sabon mataki na haɗin gwiwa a shekarar 2027 domin ƙarfafa ayyukan kirkire-kirkire.

Ministar Fasaha da Yawon Buɗe Ido ta Najeriya, Hannatu Musawa, ta kuma marabci wannan haɗin gwiwa, tana mai cewa ƙasashen biyu suna da dogon tarihi na dangantaka da burin ci gaba. Ta ƙara da cewa Najeriya na ganin dama a fannoni kamar al’adu da yawon buɗe ido, da harkokin fasaha a ƙarƙashin shirin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu.

Bangarorin biyu sun ce wannan dangantaka na nufin mayar da ra’ayoyi zuwa mafita ta zahiri da za ta taimaka wajen bunƙasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi, da inganta hidimomin jama’a a Najeriya.

0 $type={blogger}: